Jama’a barkan mu da Juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafin da ke bai wa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa da na nesa.
A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Bello Hamza, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar Juma’a tare da kai ziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka.
Sako daga Hussaina Macinama
Assalamu alaikum!
Ina mika godiyata ga ma’aikatan gidan wannan jarida mai albarka tare da sakon gaisuwata da suka ba ni damar da na mika sakon gaisuwata na gode.
Ina mika sakon gaisuwata ga iyayena da yayyena da kannena ‘yan uwana mata da maza wadanda muka yi makaranta tare da su, al’umar Musulmi baki daya duk ina yi muku fatan alkhairi tare da fatan an yi Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana, ina gaida mijina tare da yi mata fatan alkhairi da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya.
Sako daga Sadik Garba Atiku
Assalaikum alaikum!
Al’ummar Musulmi, ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyayena ina yi musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida yayye iyaye da kannensu tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da Juma’a.
Sako daga Muhammad Sani
Ina mika sakon Goron Juma’a ga al’ummar Musulmi gaba ki daya, da jamia’an tsaro dake kasar nan baki daya. Ina mika gaisuwa na ga mahaifiyata Hajiya Lamee Musa, da mahaifina Alhaji Aliyu Isah.Ina mika sakon gaisuwa na ga yaya ta Ummi, da kanwata Aisha, da yaya na Faisal, da kanina Abdulrahman, da yaya na Sadik, da fatan sakona ya iso ku cikin koshin lafiya
Sako daga Zainab Rabi’u
Ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga iyayena da fatan alkhairi ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida dana waje da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukakin Musulmi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana smin ya Allah.
Sako daga Asma’u Usman
Assalamu alaikum! Ina mika sakon gaisuwa ga ma’aikatan wannan gidan jarida na Leadership Hausa tare da mika godiya ta da suka bani dama dana mika sakon gasuwata nagode.
Ina mika sakon gaisuwa ta ga mijina da iyaye na ina fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa ta ga ‘yan ‘uwana yayyena da kannena da fatan suna cikin koshin lafiya sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Aisha Usman
Assalamu alaikum! Ina mika sako gaisuwa ta ga mutanan gidan wannan jarida mai albarka tare da mika godiya ta da suka bani dama da na mika sakon gaisuwata na gode.
Ina gaida Iyaye da ‘yan uwa da abokan arziki, abokan karatu da abokan aiki na da al’ummar Musulmi baki daya tare da barka da Juma’a da fatan an yi Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.