A baya bayan nan kasar Sin ta karbi bakuncin manyan tarukan tattaunawa masu matukar muhimmanci, wadanda ke da alaka da bunkasa wayewar kai tsakanin al’ummun duniya. Cikin tarukan akwai dandalin Nishan karo na 11 da ya gudana a Qufu, mahaifar shahararren masanin falsafar nan na kasar Sin wato Confucius. Kazalika, birnin Beijing ma ya karbi bakuncin taron koli na ministoci game da tattauna batutuwan da suka shafi wayewar kan kasa da kasa. A daya bangaren, an gudanar da taron koli na ministocin kasashe mambonin hadin gwiwa na Shanghai ko SCO a birnin Tianjin mai makwaftaka da Beijing.
A dukkanin tarukan nan da suka gudana cikin wannan wata na Yuli, shugabannin kasar Sin, da baki mahalarta masu tarin yawa daga sassan kasa da kasa, sun jaddada muhimmancin tattaunawa tsakanin mabambantan wayewar kai tsakanin al’ummun duniya, a matsayin wani ginshiki na dinke sassan kasa da kasa waje guda da cin gajiya tare.
- Sojoji Sun Kama Jami’an NURTW 2, Da Mai Karɓar Harajin IPOB
- Roy Jakobs: Ba Za A Iya Rabuwa Da Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Sin Ba
Ko shakka babu tattaunawa, da gudanar da shawarwari tsakanin mabanbantan wayewar kai na ingiza damar musayar fahimta, da akidu, da kwarewa tsakanin al’adu, da wayewar kai, da dinkewar kasashe, wanda hakan ka iya bunkasa fahimtar juna, da yaukaka hadin gwiwa tsakanin daukacin kasashen duniya.
Tattaunawa tsakanin mabambantan wayewar kai ba sabon batu ba ne. Batu ne da ya ratsa tsawon tarihin bil’adama, kuma ana iya ganin misalai da dama na hakan a gabobin tarihi daban daban. A fannin kare kimar al’adu da aka gada daga kaka da kakanni, Sin ta cimma manyan nasarori masu tarin yawa. Kuma wayewar kanta, na cikin mafiya dadewa a duniya, wanda ya wanzu har tsawon shekaru 5,000, tare da yaduwa ta hanyoyin tattaunawa, da zaman jituwa tare da sauran al’ummun duniya.
Hakan ne ma ya sa sanarwar bayan taron Beijing na ministoci game da wayewar kan duniya, ta jaddada muhimmancin musaya tsakanin al’ummu, da cudanyar al’adu a matsayin ginshikin kawar da rashin jituwa tsakanin mabambantan wayewar kai, da bunkasa hadin gwiwa wajen shawo kan tarin kalubale dake addabar duniya. Yayin da a daya hannun, tsare-tsare 110 da aka fitar yayin taron suka mayar da hankali ga yadda za a aiwatar da shirye-shiryen cimma gajiya daga mabambantan wayewar kai na sassan kasa da kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp