• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Guterres Ya Yaba Wa Kasar Sin Kan Yadda Take Kokarin Tinkarar Sauyin Yanayi

byCMG Hausa
3 years ago
Guterres

A jiya Talata, a gefen taron bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayin duniya ta MDD karon 27 (COP27) dake gudana a Sharm el Sheikh na kasar Masar, Xie Zhenhua, wakilin musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin, kana manzon kasar mai kula da batun tinkarar sauyin yanayi, da Zhao Yingmin, jagoran tawagar kasar Sin dake halartar taron COP27, kana mataimakin ministan muhalli na kasar, sun gana da babban sakataren MDD Antonio Guterres.

Yayin ganawar tasu, Mista Guterres ya yabawa kasar Sin, kan yadda take kokarin rungumar tsare-tsaren kare muhalli, da daukar hakikanan matakai, musamman ma a fannin raya bangaren makamashi da ake iya sabuntawa.

  • Kamfanin Sin Ya Haskaka Kauyen Lauteye Na Jihar Kanon Nijeriya

Guterres ya ce, yana fatan tawagar Sin za ta kara yin tasiri a taron COP27, da mu’amala tare da sauran bangarori, don samar da gudunmawa a kokarin tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya.

A nasa bangare, Xie Zhenhua ya ce, kasar Sin na kira ga bangarori daban daban da su cika alkawuran da suka dauka, da aiwatar da yarjejeniyar Paris yadda ya kamata.

Musamman ma ana fatan ganin kasashe masu sukuni sun gaggauta cika alkawarinsu na ba da tallafin dalar Amurka biliyan 100 ga kasashe marasa karfi a kowace shekara, da gabatar da tsarin rubanya kudin tallafin da ake samarwa, don karfafa amincewar juna da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu sukuni da masu tasowa.

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

A nashi jawabi, Zhao Yingmin ya nanata muhimmancin da gwamnatin kasar Sin take bayarwa kan aikin tinkarar matsalar sauyin yanayi.

Ya ce Sin na son yin aiki tare da gamayyar kasa da kasa, don daidaita wannan matsala yadda ya kamata. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Next Post
Rundunar ‘Yansanda Ta Karyata Rahoton Kai Wa Ayarin Motocin Atiku Hari A Jihar Borno

Rundunar ‘Yansanda Ta Karyata Rahoton Kai Wa Ayarin Motocin Atiku Hari A Jihar Borno

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version