Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya raba kayan aikin sana’o’i ga dalibai 1,130 da suka kammala karatu a cibiyoyin koyar da sana’o’i guda shida domin bunkasa samar da ayyukan yi da dogaro da kai.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an mika kayayyakin ne a wani biki da aka yi a ranar Asabar a gidan gwamnatin Kano.
- UADD Ta Yaba Wa Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Kan Himma Da Kishin Kasa
- NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas
Da yake jawabi a wurin taron, Gwamna Yusuf ya ce, an shirya shirin ne domin “sake fata, farfado da mafarkan alkairai, da kuma fuzgo irin kwarewa da matasa ke da shi don dogaro da kai, wacce za ta samar da sabbin hanyoyin habaka tattalin arzikin jihar.”
Ya bayyana cewa, gwamnatin da ta gabata ce ta rufe cibiyoyin da aka kafa a gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, amma gwamnatinsa ta yanke shawarar farfado da su domin magance matsalar rashin aikin yi.
“Don haka ne a yau, kowane Dalibi wanda ya kammala karatun, ba kawai takardar shaida za a bashi ba har ma da kayan aikin sana’ar da ya koya” in ji Yusuf.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp