Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa ta’aziya ga iyalan shahararren jarumin Kannywood, Abdullahi Shuaibu Karkuzu, wanda ya rasu bayan doguwar jinya.
Karkuzu ya rasu yana da shekaru 94.
- Manyan Amfanin Gona Biyar Da Ya Kyautu Manoma Su Zuba Hannun Jari A 2025
- Tinubu Ya Ba Da Umarnin Kamo Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo
Sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a a Kano, ta bayyana cewa gwamnan ya yi matuƙar alhinin rasuwar Karkuzu, wanda ya kasance babban jarumi kuma mai tallafawa ci gaban masana’antar Kannywood.
Gwamnan ya ce mutuwar Karkuzu babban rashi ne ga masana’antar, musamman wajen kawo ci gaba da nishaɗantar da al’umma.
Ya bayyana cewa marigayin ya bar babban giɓi a masana’antar, wanda ba za a iya cike sa cikin sauƙi.
A cikin shekaru da ya yi a masana’antar, Karkuzu ya nuna ƙwarewa wajen kawo canji da kuma nishaɗantar da al’umma.
A madadin gwamnatin Kano da al’ummar jihar, gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin, ‘yan Kannywood, da masana’antar.
Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya jiƙan jarumin, Ya kuma Aljanna Firdausi ta zama makomarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp