Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya bayyana hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar ta yanke a ranar Juma’a a matsayin “rashin adalci”, inda ya sha alwashin kalubalantar hukuncin a kotun daukaka kara.
Da yake mayar da martani kan hukuncin da kotun ta yanke, Gwamna Adeleke ya sauki hukunci da kotun ta yanke na ayyana dan takarar APC, Gboyega Oyetola, a matsayin wanda ya lashe zaben.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Kori Adeleke A Matsayin Gwamnan Jihar Osun
- Adeleke Ya Dakatar Da Lasisin Masu Hakar Ma’adinai A Osun
Gwamnan ya yi kira ga ‘Yan jam’iyyar PDP da magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, ya kuma sha alwashin daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara.
Adeleke, ya bayyana cewa shi ne wanda ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a Jihar ranar 16 ga watan Yuli.
“Ina kira ga magoya bayanmu da su kwantar da hankalinsu, za mu daukaka kara a kan hukuncin da aka yanke, kuma muna da tabbacin za a yi mana adalci,”
“Mu tabbatar wa da jama’armu cewa za mu yi duk mai yiwuwa don ci gaba da rike wannan matsayi na gwamna da muke kai,” in ji Gwamna Adeleke.