Gwamnatin jihar Ekiti ta amince da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikata a jihar.
Amincewar ta biyo bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar da shugabannin kungiyoyin kwadago, wacce ta bayyana cewa, sabon mafi karancin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024.
- Xi Ya Yi Kiran Gina Duniya Mai Ci Gaba Ta Bai Daya Bisa Adalci A Taron G20
- Shugabannin Sin Da Faransa Sun Rubuta Bayanai Domin Wani Bikin Baje Koli Na Musamman
Shugabar ma’aikata, Dr. Folakemi Olomojobi ce ta sanya hannu a madadin gwamnatin jihar kan yarjejeniyar, yayin da shugabannin kungiyoyin kwadago a jihar suka sanya hannu a madadin ma’aikata.
Shugabar ma’aikatan ta ce, Gwamna Biodun Oyebanji ya amince da tsarin biyan sabon mafi karancin albashin yadda kwamitin mafi karancin albashi ya gabatar da shi don ba da fifiko ga jin dadin ma’aikata.
Da take bayyana Gwamna Oyebanji a matsayin “gwamna abokin ma’aikata” wanda ke fatan alheri ga ma’aikata a jihar, Dokta Olomojobi ta yi amfani da wannan dama wajen bayyana godiyarta ga shugabannin kwadago bisa fahimtarsu, hakuri da jajircewarsu wajen ganin sun cimma nasara ga ma’aikata.
Ta kuma gode wa ma’aikatan Ekiti bisa hakurin da suka nuna kan sakamakon hukuncin da kwamitin ya yanke da kuma yadda suka amince da gwamnatin jihar.