A ranar Larabar da ta gabata ne, wakilan Gwamna Mai Mala Buni suka dankawa wakilin iyalan Sheikh Goni Aisami mukullai da takardun gidaje guda uku.
Kowacce daga cikin matan Sheikh da ‘ya’yanta za su mallaki daya, ciki harda matarsa da suka rabu amma akwai ‘ya’ya a tsakaninsu.
A kwanakin baya wani mai sharhin labaru, Audu Bulama Bukarti ya sanar da cewa, Gwamna Mai Mala yayi alkawarin siyawa iyalan Sheikh Goni Gidaje, amma da ya tashi sai ya saya musu guda uku ba biyu! ya hada harda tsohuwar Matar Sheikh da suka rabu amma akwai ‘ya’ya a tsakaninsu.
Haka kuma gwamnan ya cika alkawarin abinci da ya dauka. Wakilai sun dankawa iyalan Sheikh Goni shinkafa buhu 12 da taliya katan 20 da mai jarka 5, sai kuma atamfa guda 10.
Mun Rahoto muku a baya yadda wani soja ya harbe Sheikh Goni daga yi masa alfarmar rage hanya, sai ya ci amanarsa don ya sace motarsa amma Allah ya tona asirinsa.
Tuni dai, hukumar Soji ta kasa ta sallami maciya amana daga aikin sojin, sannan kuma ta tasa keyarsu zuwa Kurkuku, suna jiran a gurfanar dasu a gaban mai shari’a da zarar kotunan sun dawo daga hotu.