Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya jaddada baiwa sojojin Nijeriya ma su aikin samar da tsaro a jihar cikakkiyar gudunmawa da goyon baya domin kawo karshen ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram a jihar.
Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a tsakiyar wannan mako, a sa’ilin da Babban Hafsan Sojojin (COAS), Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, ya Kawo masa ziyara a fadar gwamnatin jihar dake Damaturu.
- Matatar Man Ɗangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦890
- Rashin Tsaro A Nijeriya: Gazawar Masu Mulki Ce Da Cin Amanar Kasa
Har wala yau kuma, Gwamnan ya yaba wa sojojin bisa ga jajircewarsu wajen tabbatar da samun gagarumin ci gaba ta fuskar bunkasar tsaro a fadin jihar.
Ya bayyana cewa a cikin ilihirin kananan hukumomin jihar 17 a jihar, an samu ci gaba sosai a fannin tsaro, yayin da al’umma ke ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin walwala.
“Ci gaba da aka samu ta fuskar tsaro a fadin wannan jihar ya baiwa gwamnati damar aiwatar da manufofi da tsare-tsare don inganta rayuwar al’umma ba tare da wata tangarda ba.” In ji Buni.
A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar.
A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya.
“Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS.
Hakazalika kuma, ya bayar da tabbacin cewa zai yi amfani da hazaka tare da kwarewarsa- musamman yadda a baya ya yi aiki a jihar Yobe- domin kawo karshen matsalar yan ta’adda.
Haka kuma, Janar Oluyede ya yaba wa gwamnatin jihar Yobe bisa cikakken goyon baya tare da irin yadda take tallafawa rundunar sojojin Nijeriya a kowane lokaci tare da yin kira kan ci gaba da kokarin da take na baiwa sojojin tallafin don saukaka musu ayyukan aikin yaki da matsalolin tsaro.