Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai yi jawabi a wani taro na habaka kasuwanci karo na biyar wanda AFSNET ke shiryawa.
Taron zai gudana daga ranar 4 zuwa 10 ga watan Satumba na shekarar 2025, a Cibiyar Habaka Kasuwanci (SAFEX) ta ƙasar Algeria.
- Za Mu Kare Bukatun Nijeriya A Mashigin Tekun Guinea – Shettima
- Kungiyar Kare Shirye-shiryen Tinubu Ta Nemi A Dakatar Da Shugaban Kamfanin NNPCL
Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa an gayyaci Gwamna Lawal don yayi jawabi taron na AfSNET karo na biyar a ranar 6 ga watan Satumba na 2025.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, taron zai gudana ne a gefen bikin baje kolin kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka karo na huɗu (IATF2025).
“Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Aljeriya za ta ɗauki nauyin gudanar da bikin baje kolin kasuwanci tsakanin Afirka (IATF2025) sannan kuma bankin Afreximbank tare da haɗin gwiwar Hukumar Tarayyar Afirka (AUC) da Sakatariyar Yankin Kasuwancin Nahiyar Afirka (AfCFTA) za ta shirya shi.
“Bikin baje kolin kasuwanci tsakanin Afirka (IATF2025) zai samar da wani tsari na musamman kuma mai ƙima ga ‘yan kasuwa don samun kasuwa guda ɗaya ta Afirka ga sama da mutane biliyan 1.4 tare da habaka tattalin arzikin cikin gida na sama da dalar Amurka tiriliyan 3.5 da aka samar a ƙarƙashin yankin ciniki cikin ‘yanci na Nahiyar Afrika.
Taken taron na bana shi ne; ‘Ƙarfin Cikin Gida, Tasirin Duniya: Ƙarfafa gwamnatocin ƙasashen Afirka masu cikakken iko don samun ci gaba mai ɗorewa, yana nuna haɗin gwiwarmu don ba da damar gudanar da mulki na cikin gida don samun sakamako mai kyau na nahiyar.
“Sakamakon nasarar taron AfSNET karo na huɗu da aka gudanar a Kisumu na ƙasar Kenya, wanda ya tara gwamnoni sama da 45, magadan gari, shugabannin ƙananan hukumomi, masu zuba jari, da kuma abokan ci gaba daga ko’ina a nahiyar Afirka, taron na AfSNET ya jaddada muhimman dabaru na ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa wajen inganta kasuwanci cikin ‘yanci na nahiyar Afrika (AfCFTA).
“Taron ya gabatar da manyan tattaunawa, zaman zurfafa zuba jari, da hada-hadar B2B da B2G, wanda ya baiwa ‘yan ƙasashe damar gabatar da shirye-shiryen ci gaba da kuma gano hanyoyin samar da kuɗaɗe.
“Tare da mai da hankali sosai kan ci gaba da haɗin gwiwar yanki, taron na Kisumu ya kasance wani muhimmin dandali na tattara albarkatu da ƙarfafa haɗin gwiwa, da tsara hanyoyin da za a iya aiwatarwa da ajandar kasuwanci da ci gaban Afirka daga tushe.”
“An gayyaci Gwamna Lawal don yayi jawabi akan muhimmin abu cikin tattaunawar da za’ayi lura da ƙwarewar sa akan tattalin arziƙi da shugabanci.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp