Yayin da gwamnan jihar Kano mai barin gado ya fara shirin fice wa daga kan karagar mulki, Abdullahi Ganduje ya roki gafarar wadanda ya bata ma wa a yayin gudanar da aikinsa na jihar a matsayin shugaba.
Sai dai, a wani martani da ya mayar ga Gwamna Ganduje mai barin gado, tsohon kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa, Muaz Magaji ya ce “Eh na yafe maka, amma ba zan taba mantawa da yadda kuka kulla makarkashiyar kawar da ni daga doron kasa ba a lokuta daban-daban”.
Ana sa ran Gwamna Ganduje zai kammala wa’adinsa na biyu na shekaru takwas nan da wata guda tare da mika ragamar shugabancin ga zababben Gwamna, Abba Kabir Yusuf.
Ganduje ya nemi yafiyar ne yayin wata lakcar watan Ramadana a Masallacin Juma’a na Al Furqan da ke Nassarawa GRA Kano ya ce “ku gafarta mini na yafewa kowa”.