Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayar da gudummawar kudi naira miliyan 10 ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin da ya afku ga ‘yan bikin Ista (Easter) a karamar hukumar Billiri.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, wani direban babbar mota ya kutsa cikin gungun mabiya addinin kirista a ranar Litinin din da ta gabata inda suke gudanar da muzahara a ranar Ista inda mutane biyar suka mutu, wasu da dama kuma suka samu raunuka.
- Yanzu-yanzu: Gwamnan Delta Oborevwori Ya Fice Daga PDP Zuwa APC
- Sabbin Haraji: Yadda ‘Yan Bindiga Ke Tilasta Wa Jama’a Biyan Miliyoyin Kuɗi A Zamfara
Gwamnan ya sanar da bayar da tallafin ne a ranar Laraba a lokacin da ya kai ziyarar jaje a karamar hukumar Billiri domin jajanta wa jama’a da iyalan wadanda abin ya shafa.
Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa.
Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2 kowanne ga iyalai biyar da suka rasa rayukan ‘yan uwansu, wanda ya kai adadin zuwa Naira miliyan 10.
Ya kuma yi alkawarin biyan kudaden jinya ga wadanda ke karbar magani a Asibitocin jihar.
A yayin da yake godiya, Sarki Maiyamba ya ce, hatsarin na Easter ya girgiza daukacin masarautar Tangale, amma ya amince da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, wanda ya ce hakan ya taimaka wajen hana barkewar rikici a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp