Gwamnan Jihar Gombe, kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya nuna alhini da jimami bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Sa’eed Hassan Jingir.
Sheikh Sa’eed Jingir, wanda ya kasance Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatissunnah (JIBWIS), ya rasu da safiyar ranar Alhamis a Jos bayan fama da rashin lafiya.
- Asusun Ajiyar Nijeriya Na Ketare Ya Ragu Da Dala Biliyan Biyu A 2025
- NPA Za Ta Sauya Mazaunin Na’urar Tantance Jiragen Ruwa Da Ke Apapa
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa wannan babban rashi ne ga al’umma da ƙasa baki ɗaya.
Ya ce marigayin ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaɗa addinin Musulunci, ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai, da fahimtar juna a cikin al’umma.
“Muna cikin matuƙar alhini da jimami bisa wannan babban rashi. Sheikh Sa’eed Jingir ya kasance malami mai hikima da jajircewa, wanda koyarwarsa ta zaman lafiya da haɗin kai za su ci gaba da zama abin koyi,” in ji Gwamnan.
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, shugabannin Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatissunnah, musamman Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, da duk al’ummar Musulmi gaba ɗaya.
Daga ƙarshe, ya yi addu’a ga Allah da ya gafarta wa marigayin, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdausi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp