• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Lawal Ya Jaddada Aniyar Inganta Kiwon Lafiya A Jihar Zamfara

Ya Ƙaddamar Da Babban Asibitin Gusau Da Aka Gyara

by Sulaiman
5 months ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirinsa na sake farfaɗo da tsarin kiwon lafiya a Jihar Zamfara, tare da cika alƙawarin gwamnatinsa na samar da nagartacce kuma ingantaccen kiwon lafiya ga al’umma.

Gwamnan ya ƙaddamar da Babban Asibitin Gusau da aka gyara ciki-da-bai a ranar Juma’a.

  • Shugaban Senegal: Ana Fatan Ci Gaba Da Zurfafa Zumuncin Dake Tsakanin Sin Da Senegal
  • Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Kassara Kamfanonin Fasaha Da Na AI Na Sin

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa gyaran babban asibitin ya haɗa da sashin kula masu haɗurra da masu neman buƙatar kulawar gaggawa, sashen kwantar da mata masu juna biyu, ɗakunan haihuwa, sashin gudanarwar asibitin, ɗakin kula da yara, da kuma sashin kula da jarirai na musamman (SCBU).

Sauran sassan da aka gyara da kuma sanya kayan aiki sun haɗa da bangaren mata masu juna biyu tiyata, wurin zama jira, ɗakin kula da mata, babban ɗakin tiyata, sashen gwaje-gwaje na Radiology, sashen kula da ƙashi, sashen GOPD, da sashen kula da kunne, maƙogwaro, ido da harkar haƙori.

Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote 

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

A lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa da hawansa mulki a watan Mayun 2023, ya ci karo da tsarin kiwon lafiya da ya tabarbare saboda rashin kulawa.

Ya ce, “Gwamnatinmu, ƙarƙashin ginshiƙan shirye-shiryen ceto, nan da nan ta fara tantance abubuwan da asibitoci ke buƙata, inda sakamakon ya zama abin tsoro kuma ya nuna akwai jan-aiki.

“Alal misali, a jihar da ke da mutane kusan miliyan 6 tare da tarin ƙalubale, na’urar duban ɗan tayi ɗaya ce kawai a cikin dukkan cibiyoyin da gwamnati ta mallaka, kuma shi ma duk faci ne a jikinsa da salataf ko’ina! Nan take na ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya don dawo da ababen more rayuwa, samar da kayan aiki a asibitocinmu tare da samar da kwarin gwiwa da horarwa ga ƙwararru a fannin kiwon lafiya.

“Don inganta ayyukan more rayuwa, mun kuma ba da kwangilar samar da kayayyaki, sakawa, gwadawa, da horar da ma’aikata kan yadda za su yi amfani da na’urorin na zamani.

“Kamar yadda aka saba a wannan gwamnati ta Jihar Zamfara, muna tabbatar da cewa duk kayan aikin da aka kawo da kuma sanya su sun kasance masu inganci kuma sun cika ƙa’idojin da ake da su.

“Bari in jaddada cewa wannan ƙaddamarwar wani bangare ne na sake fasalin jihar Zamfara bakiɗaya a fannin kiwon lafiya, za ku iya tuna cewa mun riga mun samar da manyan asibitocin da aka gyara a garuruwan Ƙaura, Maradun, Maru, da Nasarawa Burkullu.

Zamfara

“Har ila yau, ana shirin ƙaddamar da wasu muhimman asibitocin da suka haɗa da Asibitin Ƙwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura, Gusau, Babban Asibitin Talata Mafara, Shinkafi, da Babban Asibitin Tsafe, da dai sauransu.

“Bugu da ƙari, bayan amincewar majalisar zartarwa ta jiha, Ma’aikatar Lafiya ta fara aikin samar da cikakken kayan aiki ga manyan asibitocin da ke Anka, kuma wannan ya haɗa da samar da kayan aiki na zamani tare da horar da ma’aikatan kiwon lafiya.

“Ya ku ’yan uwa maza da mata, waɗannan ayyukan suna nuna hangen nesan mu na gina tsarin kiwon lafiya na zamani, mai aiki da kuma ɗorewa wanda zai rage yawan tura marasa lafiya zuwa wasu asibitoci a wajen jihar tare da tabbatar da cewa ’yan jihar mu sun sami ingantaccen kulawa kusa da gida.

“Yayin da muke murnar wannan nasarar, ina so in jawo hankalin mahukuntan asibitin kan buƙatar yin taka-tsan-tsan wajen amfani da kuma kula da wannan wuri.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnati Za Ta Fara Sayar Wa Ɗangote Ɗanyen Mai Da Naira A Watan Oktoba
Labarai

Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote 

October 27, 2025
An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 
Labarai

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

October 27, 2025
Zamfara
Labarai

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Next Post
Gwamnatin Tarayya Na Ƙoƙarin Magance Yawan Soke Tashin Jirage Da Jinkiri A Nijeriya

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.