Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jaddada cewa yaƙi da matsalolin tsaro a jihar aiki ne na haɗin kai da ya rataya a wuyan kowa da kowa, ba na gwamnati kaɗai ba.
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Litinin 20 ga watan Oktoban 2025 yayin da gwamnan ya jagoranci zama na 18 na Majalisar Zartarwa ta Jihar Zamfara a Gidan Gwamnati da ke Gusau, inda aka tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi tsaro, ilimi, kiwon lafiya da kuma ci gaban gine-gine a faɗun jihar.
A jawabin buɗe taron, Gwamna Lawal ya ce, “Ina so na tunatar da mu duka cewa yaƙin da muke yi da rashin tsaro babban nauyi ne na haɗin kai. Mun samu nasarori da dama, inda muka farfaɗo da zaman lafiya a yawancin yankuna na jihar. A yau, barazanar ’yan bindiga ta ragu matuƙa idan aka kwatanta da shekarun baya.”
Gwamnan ya kuma buƙaci mambobin majalisar da su kasance masu aiki da faɗakarwa, su kasance kusa da jama’ar yankunansu da kuma shugabannin ƙananan hukumomi. Ya umarce su da su riƙa isar da rahotanni na yau da kullum ga Kwamishinan Tsaro, tare da yin addu’a ga waɗanda suka rasa rayukansu wajen kare al’umma da zaunar da zaman lafiya a jihar.
Bugu da ƙari, Gwamna Lawal ya ƙarfafa mambobin majalisar su ƙara haɗin kai da sauran jami’an gwamnati domin tabbatar da ingantacciyar tafiyar da al’amuran mulki da gudanar da ayyukan ci gaba cikin nasara.














