Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Dare Lawal, ya bayyana kaɗuwarsa bayan samun rahoton kisan jami’an tsaro takwas da ’yan bindiga suka yi a hanyar Funtuwa zuwa Gusau.
Rahoton ya bayyana cewa, harin ya shafi jami’an ‘yansanda da Askarawan Zamfara.
A shafinsa na Facebook, Gwamna Lawal ya rubuta: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Na samu rahoto mara daɗi na kwanton ɓauna da ’yan bindiga suka yi wa jami’an tsaron ’yansanda da Askarawan Zamfara a hanyar Funtuwa zuwa Gusau, inda suka kashe jami’ai takwas. Allah (T) Ya jiƙan su, Ya bai wa iyalai da ’yan uwan haƙurin wannan rashi.
“Muna roƙon Allah (T) Ya kawo mana ƙarshen wannan matsala ta tsaro a duk faɗin Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.”
Lamarin ya jawo damuwa daga al’umma da shugabannin siyasa, yayin da hukumomin tsaro ke ƙara ƙoƙari wajen gano waɗanda suka aikata wannan mummunan laifi da tabbatar da zaman lafiya a yankin.