Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya nuna alhininsa bisa rasuwar Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Kauran Namoda ta Kudu.
Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar da wata sanarwa inda ya ce gwamnan ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da shugabannin majalisar dokokin jihar.
- Sin Ta Kara Wasu Kamfanonin Amurka 12 Cikin Jerin Wadanda Ta Dakatar Da Fitar Musu Da Wasu Kayayyaki Daga Kasar Sin
- Yadda Kasashen Afirka Za Su Iya Rage Illar Harajin Amurka
A cewarsa, gwamnatin jihar ta aike tawaga ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamna, Mallam Mani Mummuni, domin halartar jana’izar marigayin a Kauran Namoda.
Sanarwar ta ce: “A madadin gwamnatin jihar, muna miƙa sakon ta’aziyya ga Shugaban Majalisar, mambobin majalisar, iyalan marigayin da kuma ɗaukacin al’ummar Kauran Namoda ta Kudu.”
Ya ƙara da cewa a wannan lokaci na baƙin ciki, gwamnati na addu’a Allah Ya bai ws iyalan marigayin ƙarfin zuciya da juriyar rashin nasa.
“Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.”