Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya amince da fara biyan Naira 70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake kaddamar da sabuwar majalisar ma’aikata ta jihar Edo a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu.
A cewarsa, mafi karancin albashin da aka dade ana tsumayi, zai fara aiki a ranar 1 ga Mayu, 2024.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp