Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya amince da bai wa ma’aikatar Jihar Katsina goron sallah naa naira 15,000 don gudnar da shagulgulan Sallar layya.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Gwamnan Raddan ya wallafa a shafinsa na X (Twitter), inda ya ce sakamakon yanayin matsin rayuwa da ake ciki, ya amince da bayar da goron Sallah na naira 45,000 ga ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi.
- Ba Zan yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba, Cewar Dikko Radda
- Dikko Radda Ya Ba Alhazan Katsina Su 4,634 Kyautar Miliyan ₦278 A Kasar Saudiyya
Gwamnan ya ce ”Naira 30,000 daga cikin kuɗin zai kasance a matsayin bashi ne da gwamnati ta ba su, inda za su biya cikin wata uku masu zuwa, inda za a riƙa cire naira 10,000 a cikin albashinsu a kowane wata daga Yuli zuwa Satumba”, cewar sanarwar.
Radda ya ce ya yi sun dauki wannan matsayar ne don taimaka wa ma’aikata haziƙan ma’aikatan jihar don su samu sukunin gudanar da shagulgulan bukukuwan babbar sallah cikin walwala da nishadi, saboda da halin matsi da ake ciki a halin yanzu.