Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kaddamar da wasu kananan asibitoci guda biyar da aka tsara su acikin manyan Motoci domin gudanar da ayyukan jinya ga al’umma.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakiyarsa, Dakta Hadiza Balarabe, ta ce, motocin da aka kaddamar za su inganta harkokin kiwon lafiya da inganta walwala da rayuwar al’ummar jihar Kaduna.
Sanata Uba Sani ya ce, asibitin ta tafi da gidanka zai yi ayyuka da dama da suka hada da kula da lafiyar Mata masu juna biyu da Jarirai da Yara, akwai na’urar haske ta binciken lafiya da duk wani bincike na dakin gwaje-gwaje na cututtukan da suka hada da zazzabin cizon sauro, HIV, Hepatitis B da C, tarin fuka da dai sauransu.
Tun da farko, shugabar ofishin kungiyar UNICEF ta Kaduna, Gerida Birukila, wadda ta yi magana a madadin UNICEF, WHO da sauran kungiyoyin samar da ci gaban al’umma sun taya gwamna Uba Sani murnar cika kwanaki 100 a kan karagar mulki, sun kuma jinjina masa kan ayyukan ci gaba da ya ke kawo wa jihar Kaduna.
Shugabar ta yabawa gwamnatin jihar bisa kaddamar da asibitoci akan motoci na tafi da gidanka domin kula da marasa lafiya, inda ta ce, hakan zai kai ga mutane da dama da ba su da damar zuwa ganin Likita sun amfana da tsarin wanda zai inganta lafiyarsu.