Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi kira ga waɗanda suka isa yin rijistar katin zaɓe a jihar, da su shiga rijistar da hukumar zabe ta ke gudanarwa a fadin kasar nan.
Gwamnatin ta bayyana wannan mataki a matsayin muhimmin lokaci na ƙarfafa dimokuraɗiyya da gina shugabanci mai ɗaukar kowa da kowa.
- DSS Ta Ba Sowore Mako Ɗaya Ya Janye Maganarsa Kan Tinubu
- Xi Ya Halarci Taron Kungiyar BRICS Ta Yanar Gizo
A wata sanarwar manema labarai , Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa “Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna ya bayar da umarni cewa ba wani ɗan ƙasa mai cancanta da ya kamata a bar shi a baya a wannan muhimmin aikin. Wannan ba kawai batun shiga cikin rajista ba ne; yana da nasaba da kare haƙƙin dimokuraɗiyya na jama’ar mu da kuma zurfafa shugabanci na gaskiya wanda ke ɗaukar kowa da kowa.”
“Don haka, Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki kafada da kafada da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hukumar Harkokin Addinai, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da cewa wayar da kai da kuma tura saƙon rajista ya isa kowace mazaba, ƙauye, da unguwa a fadin Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki.
Kwamishinan ya ƙara da cewa jagorancin Gwamnan na bai wa haɗin kan al’umma muhimmanci a matsayin ginshikin shugabanci na dimokuraɗiyya.
“Wannan ƙoƙarin wayar da kai yana nuna hangen nesa na Gwamna na gudanar da mulki mai maida hankali kan bukatun jama’a, inda kowace murya ke da muhimmanci, kuma kowane ɗan ƙasa yana da rawar da zai taka wajen gina makomar Jihar Kaduna.
“ Muna kira ga duk masu ruwa da tsaki — shugabannin al’umma, ƙungiyoyin matasa, ƙungiyoyin mata da kuma masu fafutukar ci gaban al’umma da su mara wa wannan yunkuri baya domin ganin an cimma nasara tare.” Inji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp