Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani a ranar Asabar ya kaddamar da aikin gina sabon titi mai tsawon kilomita 18 da zai hade kananan hukumomin Sanga da Kafanchan da ke jihar.
Sabuwar hanyar za ta hade manyan kananan hukumomin biyu na Kudancin Kaduna, ta hanyar Kiban da Godogodo domin rage doguwar tafiyar da ke tsakanin kananan hukumomin biyu, wanda hanyar da ta ke bi ta Fadan Karshi da Gidan Waya ta kai kilomita 62.
- MDD Ta Yi Maganar Rayuka 190 Da Aka Kashe A Filato
- Yadda Tasirin Sauyin Yanayi Ke Shafar Yankuna A Jihar Yobe
Da yake kaddamar da aikin, Gwamna Uba Sani, ya ce sabuwar hanyar Sanga zuwa Jema’a, na daya daga cikin ayyukan da gwamnatinsa ta yi na kawo sauyi a yankunan karkara da nufin farfado da tattalin arzikin karkara da kuma cike gibin ci gaban da ke tsakanin yankunan karkara da biranen jihar.
Gwamnan, yayin da yake tabbatar da cewa, gwamnatinsa za ta tabbatar da ci gaban dukkan sassan jihar, ya ce, gwamnatinsa ta himmatu wajen cika alkawarin da ta dauka na raya karkara ta hanyar inganta ababen more rayuwa.