Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana jin dadinsa kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar ta yanke, wanda a cewarsa ya ce kotun ta tabbatar da nasararsa a ranar Alhamis a shari’ar zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
A baya LEADERSHIP ta bayar da rahoton cewa kotun za ta yanke hukuncin ne ta manhajar Zoom saboda yanayin tsaro.
- Kotun Zabe Ta Ce Zaben Gwamnan Kaduna Bai Kammalu Ba (Inconclusive)
- ‘Yan Fashin Daji Sun Kai Wani Sabon Hari Sun Kashe Mutum 6 A Yankin Kudancin Kaduna
Jim kadan bayan kotun mai alkalai uku ta yanke hukuncin, dan takarar jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani, ya bayyana farin cikinsa kan hukuncin da kotun ta yanke, ya kuma yaba wa abokin takararsa Isah Ashiru Kudan na jam’iyyar PDP da ya yi kokensa ta hanyar da doka ta tanada.
“Ina yabawa dan uwana, Hon Isah Ashiru Kudan, da ya garzaya kotun don kai kokensa, wannan ya nuna karara irin tasirin da dimokuradiyya da kuma wayewa a tafarin tafiyar da siyasa.
“Ina kira ga Hon Isah Ashiru da ’yan jam’iyyar adawa a Jihar Kaduna da su ba mu hadin kai a kokarin da muke na ciyar da jiharmu gaba zuwa wani matsayi mai girma, dukkanmu masu ruwa da tsaki ne a kudurin gwamnatinmu na PROJECT KADUNA. Ina fatan mu hada hannu wajen magance dimbin kalubalen da ke addabar jihar.
“Ina kira ga ‘yan jam’iyyarmu ta APC da su gudanar da murnar wannan nasara cikin lumana.”