Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya mika takardar neman amincewar Majalisar dokokin jihar kan bukatar kafa cibiyar yaki da cututtuka ta jihar Kano.
Hakan na kunshe ne acikin wata takarda da shugaban majalisar, Jibril Isma’il Falgore ya karanta a zauren majalisar a ranar Litinin.
Wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Majalisar, Uba Abdullahi ya fitar, ta ce, wani bangare na cikin wasikar ya bayyana cewa; “idan aka kafa cibiyar za ta yi gaggawar magance bullar cututtuka da ke yawan barkewa a Jihar.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp