Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga Hukumar kula da kafafen Yada Labarai ta Kasa (NBC) da ta yi doka kan gidajen rediyo da talabijin na yanar gizo, inda ya yi gargadin cewa “labaran da ba a tantance ba, kuma masu tayar da hankali” da ke yawo a kafafen sada zumunta, na barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a taron Africast 2025 da aka yi a Legas, wanda hukumar NBC ta shirya wanda ya samu halartar kwararru kan harkokin yada labarai, masu tsara manufofi, da masu ruwa da tsaki a masana’antar yada labarai.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Mustapha Muhammad ya fitar, Gwamna Yusuf wanda ya samu wakilcin babban daraktan yada labaransa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake samun karuwar amfani da kafafen yada labarai na zamani wajen yada labaran da ba a tantance ba.
Gwamna Yusuf ya lura cewa, wasu kafafen yada labarai na yanar gizo suna amfani da manhajojin su wajen yada “labarai masu raba kan addini da siyasa,” wanda a cewarsa, za su iya gurgunta hadin kan al’umma da kwanciyar hankali idan ba a magance su ba.