Jihar Kano ta zama jihar da ta fi kowace jiha samun kyakkyawan sakamako a jarrabawar kammala sakandare ta shekarar 2025 (SSCE) da hukumar shirya jarabawar ta kasa (NECO) ta gudanar, nasarar da gwamnatin jihar ke dangantawa da sauye-sauyen da ake yi a fannin ilimi.
Kano ce ke kan gaba a jadawalin ɗaliban da suka yi nasara a jarabawar, da mutane 68,159, Legas ta biyo da mutane 67,007, yayin da Oyo ta zo na uku da mutane 48,742.
- ’Yansanda Sun Kama Sojan Gona Da Motocin Sata 3 A Jigawa
- Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku
Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya nuna jin daɗinsa ta bakin mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana nasarar a matsayin jajircewar gwamnatinsa a fannin ilimi.
A cewarsa, jihar ta ba da fifiko wajen samar da kudade, kayayyakin more rayuwa, da kuma samun damar koyo tun bayan hawansa kujerar mulki.
Gwamnan ya kara da cewa, yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali kan ilimin ’ya’ya mata, bayar da tallafin karatu, da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, ya taimaka wajen kawo sabon matsayi a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp