Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da aikin gina titi mai tsawon kilomita 7.1 daga shataletalen Terminus zuwa Molai, tare da aikin ginin gadar sama, wadda ita ce gadar sama ta hudu a jihar, da za ta ratsa Post Office da ke cikin birnin Maiduguri, a ranar Talata.
Wadannan ayyuka an tsara aiwatar dasu ne domin magance matsalar cunkoson ababen hawa, tare da saukaka harkokin zirga-zirgar ababen hawa da na jama’a, ayyukan da za su inganta tattalin arzikin jihar.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutum 8 Kan Zargin Kashe Jariri A Borno
- Gwamnan Edo Ya Dakatar da Sarki Saboda Matsalar Tsaro A Yankinsa
Ana sa ran za a kammala aikin nan da watanni 8 zuwa 10, aikin hanyar zai kawo ci gaba ga daruruwan ma’aikata tare da masu neman na-kansu a tattalin arzikin jihar.
A jawabin Gwamna Zulum wajen kaddamar da aikin titin, ya ce, “A ci gaba da tsarinmu na sabunta birane, a yau mun kaddamar da gina titi mai tsawon kilomita 7.1 daga tashar borno Express zuwa Molai, hadi da karin ginin gadar sama ta hudu.
“Abin da muke da burin aiwatar wa, shi ne ba don kawai kyawawan ayyuka ba, har ma don daukar nauyin ci gaban al’ummar Maiduguri, kuma ya zama dole mu fadada birnin Maiduguri.”
Gwamna Zulum ya yi kira ga yan kwangilar su tabbatar da bin ka’idojin inganci da kuma kammala aikin a cikin lokacin da aka kayyade.
“Za a kammala aikin cikin watanni goma, an bayar da kwangilar kan naira biliyan 16, kuma mun biya kashi 50% na wannan adadin kudin. Don haka, muna kira ga yan kwangilar cewa, ba su da wani uzuri na bata lokacin aikin. Mun kuma ajiye sauran Naira biliyan 8, za a biya a lokacin da aikin ya kammala.” In ji Zulum.
A nashi bangaren, Kwamishinan Ayyuka da Gidaje a jihar borno, Injiniya Mustapha Gubio, ya bayyana cewa, gadar saman za ta hada sabuwar hanyar ta bangarorin biyu na kogin Ngada-bul.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta sa ido kan ayyukan, tare da tabbatar da bin dukkan ka’idojin kwangila.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp