Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Gida-gida, ya rushe dukkan jami’ai da nade-nade da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi a Jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda dauke da sa hannunsa, inda tace “duk wani wanda Ganduje ya yi wa nadin siyasa, musamman shugabannin Hukumomin Gwamnati da kamfanoni, su ajiye aiki nan take” kamar yadda Premium Times Hausa ta rahoto.
Ya kuma rushe hukumomin gudanarwar dukkan kamfanoni da cibiyoyi da manyan makarantu.
Abba ya umarci jami’an tsaro da su karbe duk wasu kadarorin gwamnatin Jihar Kano, wadanda aka sayar a lokacin mulkin Ganduje.
Haka nan kuma, ya kafa Hukumar Tsaftace Mullahi wadda ya ce nan ba da jimawa ba zai kaddamar da ita.