Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ya yi alkawarin fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000 ga ma’aikatan jihar daga Oktoba, 2024.
Ya kuma jaddada cewa, ilimi kyauta ne a duk makarantun gwamnati da suka hada da firamare da karamar sakandire da babbar Sakandire a jihar.
- Jihar Kano Ce Za Ta Fara Aiwatar Da Sabon Mafi Karancin Albashi – Gwamna Yusuf
- Mun Kaɗu Matuƙa Kan Labarin Mutuwar ‘Yan Mauludi A Hanyar Saminaka – Gwamnan Kaduna
Gwamna Soludo ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Cibiyar Raya Mata ta Farfesa Dora Akunyili, Awka yayin da yake ganawa da manyan malamai da shugabannin makarantun firamare da sakandare na gwamnati da ke jihar.
Soludo wanda a baya ya ayyana ilimi kyauta a makarantun firamare da karamar sakandire na gwamnati, ya kara da cewa, “Daga mako mai zuwa, tsarin ilimi kyauta ne ga manyan dalibai a duk makarantun gwamnati a Anambra.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp