Gwamnan babban bankin kasar Sin, Pan Gongsheng, ya halarci taron kwamitin kula da al’amuran kudi na duniya (IMFC) karo na 51 a birnin Washington, inda ya gabatar da jawabi.
A jawabin nasa, Pan ya jaddada cewa, halin da ake ciki yanzu haka game da ci gaban tattalin arzikin duniya ba shi da karsashi, kuma yana fuskantar kasadar rugujewa, domin karin harajin kwastam na cin zarafi da Amurka ta yi a baya-bayan nan ya yi matukar keta hakkoki da muradun sauran kasashe, da yin zagon kasa ga tsarin shugabancin da ake damawa da kowa da kowa, kana ya haifar da babbar illa ga tsarin tafiyar da tattalin arzikin duniya, ya kuma kawo cikas ga kwanciyar hankali da samun bunkasar tattalin arzikin duniya da aka dade ana morewa.
Ya ci gaba da cewa, ya kamata cikin gaggawa kasashe su karfafa tsara manyan manufofin tattalin arziki, da nuna goyon baya ga tsarin cinikayyar bangarori masu yawa, da sa kaimi ga dunkulewar ci gaban tattalin arzikin duniya da za ta kasance a sarari, da ta hade kowa da kowa, mai amfanarwa ta bai-daya, tare da daidaita alkibla, da kuma kiyaye tafiyar da tattalin arziki da hada-hadar kudi ta duniya baki daya cikin kwanciyar hankali.
Kazalika, ya ce, kasar Sin tana son kara zurfafa hadin gwiwa tare da IMF wato asusun ba da lamuni na duniya, da kuma ba shi goyon baya wajen taka muhimmiyar rawa a kan kiyaye tafiyar da tattalin arziki da hada-hadar kudin duniya cikin kwanciyar hankali.
Bugu da kari, Pan ya jaddada bukatar gaggauta zurfafa sauye-sauyen asusun na IMF a bangaren kaso, yana mai bayyana gyare-gyaren da suka kamata a yi a bangaren rabon kason a matsayin wani muhimmin bangare na sake fasalin tsarin shugabancin IMF. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp