Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya sallami Hajiya Zainab Baban Takko daga kan muƙaminta na Kwamishinar kula da harkokin mata da jin daɗin yara ƙanana.
Matakin na ɗauke ne cikin wata sanarwar da babban mashawarcin gwamnan kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Mukhtar Gidado, ya fitar a jiya, inda ya tabbatar da cewar sallamar ta fara aiki nan take ba tare da ɓata lokaci ba.
- Gwamnan Bauchi Ya Gargaɗi Magoya Bayan Wike A PDP
- Majalisa Ta Daƙile PENGASSAN Akan Shirin Daina Kai Wa Matatar Ɗangote Gas Da Ɗanyen Mai
Gidado ya bayyana matakin a matsayin wani ɗan ƙaramin garambawul ga majalisar zartarwa ta jihar.
Babu wani dalilin da aka bayar na korar Kwamishinar, sai dai gwamnan ya gode mata bisa gudunmawar da ta bayar tare da mata fatan alkairi a rayuwarta ta gaba.
LEADERSHIP ta labaro cewa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya rantsar da Hajiya Zainab Baban Takko a matsayin Kwamishina ne a ranar 9 ga watan Satumban 2024 tare da wasu sabbin kwamishinoni biyu.
Kafin ta hau kan wannan kujerar, ta zama shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Bauchi wanda gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya naɗa ta a watan Yulin 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp