Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya sassauta dokar hana fita na awanni 24 da ya kakaba a karamar hukumar Katagum biyo bayan tabarbarewar lamarin tsaro da aka samu a yayin zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da yunwa a garin Azare.
Gwamnatin ta sassauka dokar daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safiyar kowace rana domin bai wa jama’a damar gudanar da harkokinsu na yau da gobe.
- Ndume Ya Ba Ganduje Haƙuri Kan Kalaman Da Ya Yi Kan Tinubu Da Suka Yi Sanadin Sauke Shi
- Gwamnatin Nasarawa Ta Amince Da Biyan 70,000 Mafi Karancin Albashi
Barista Ibrahim Muhammad Kashim, sakataren gwamnatin jihar (SSG) ne ya sanar da hakan a daren ranar Talata, inda ya ce, gwamnatin jihar da hukumomin tsaro bayan nazartar lamarin, sun gano cewa, an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Idan za a tuna dai, gwamnatin ta kakaba dokar hana zirga-zirga na awanni 24 a karamar hukumar Katagum ne bayan da aka samu wasu matasa da lalata kadarorin jama’a da sace-sace da sunan zanga-zangar matsin rayuwa a ranar Litinin a garin Azare.
Sanarwar da Kashim ya fitar ta ce, bisa saukaka wa jama’a da ba su damar komawa harkokinsu na yau da kullum ne ya sanya gwamnan amincewa da sassauta dokar.
Kan hakan, gwamnan ya bukaci jama’a da a kowani lokaci suke bai wa hukumomin tsaro hadin Kai domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.