Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya gargaɗi jami’an ma’aikatar lafiye da safiyo ta jihar Bauchi da jami’an ƙaramar hukumar Darazo da shugabannin gargajiya da dangane da bayar da filayen da aka ware domin yin kiwo don manoma su yi noma.
Gwaman ya yi wannan kiran ne ranar Lahadi a lokacin da ya je Darazo domin sulhunta rikicin manoma da makiyaya wanda ke neman zama babbar matsala a garin na Darazo, biyo bayan rikicin baya-bayan nan da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya da ya janyo jikkata mutane da dama da rasa ababan hawan su.
- Gwamnatin Bauchi Ta Cire Shugaban Makaranta Kan Satar Kayan Gwamnati
- Kotu Ta Umarci Gwamnatin Bauchi Ta Biya Tsohon Akanta-Janar Naira Miliyan 100
Gwamnan ya nuna damuwarsa kan rikicin da ake samu wajen amfani da filaye, musamman mayar da wuraren da aka ware domin kiwo zuwa gonaki, ya lura da cewa yin noma a kan filayen da gwamanti ta ware domin kiwo ne musabbabin janyo rashin jituwa a tsakanin manoma da makiyaya.
Ya yi bayanin cewa Darazo ta zama ɗaya daga cikin yankunan da suke samar da amfanin gona sosai a shiyyar Bauchi ta tsakiya, amma rikicin cikin gida tsakanin manoma da makiyaya na neman janyo damuwa, don haka ya nemi juna da su kai zuciya nesa.
A cewar Bala Muhammad sakamakon yawan bukatar da jama’a suke da shi kan filin noma, ya sanya gwamnatin ta ware filaye masu nisan hekta 2,500 domin harkokin noma. Lamarin da makiyaya suke ganin kamar zai shafi harkokin kiwonsu.
Domin neman mafita da samar da zaman lafiya mai ɗaurewa, gwamnan ya kafa kwamiti na musamman da zai hhaɗa ukkanin bɓangarorin da abin ya shafa da jami’an gwamnati domin daddale asalin filayen da aka ware domin noma da ware iyakokin noma da kuma na kiwo domin tabbatar da adalci da gaskiya a tsakanin kowane ɓangare.
Gwamnan ya jaddada cewa dukkanin ɓangarorin biyu na manoma da makiyaya kowa na da rawar da yake takawa wajen ci gaban tattalin arziki, don haka ya nemi a mutunta juna a zauna lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp