Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya gargadi Nijeriya da sauran kasashe masu tasowa da su yi taka-tsan-tsan kan hadarin bashi, yana mai cewa idan ba a magance su ba za su kawo cikas ga ci gaba n tattalin arziki da wadata.
Gwamnan CBN ya kuma ce a halin da Nijeriya ke ciki na gaf da shiga hatsarin basuka, duba da halin da kasuwan duniya ke ciki da kuma karuwar basuka da ya samu asali tun daga barkewar cutar Korona.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Abinci A Jihohi
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Kara Gina Madatsun Ruwa Domin Noman Rani
Masana da dama dai sun jima suna yekuwar cewa tulin basukan da Nijeriya ke kai ne suka zama asasin matsalolin tattalin arziki da ke kara haifar da matsaloli a kasar nan musamman na matsin rayuwa.
Duk da basuka masu yawa da ake bin Nijeriya na ciki da waje, har yanzu jagororin kasar a matakin tarayya da jihohi na ci gaba da kinkimo wa kansu basuka.
Lamarin da ke kara maida al’umman kasar cikin mummunn talauci da fatara, musamman tun bayan cire tallafin man fetur a farkon hawan wannan gwamnatin da kuma karyewar darajar naira.
Sai dai Cardoso ya ce, hatsarin da babban bankin duniya da asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) suka bayyana, na nuni da cewa Nijeriya na fuskantar barazana.
Ya shaida hakan ne a Abuja lokacin kaddamar da taron masu ruwa da tsaki kan basuka na bankin duniya, IMF, (WAIFEM).
Ya samu wakilcin daraktan tsare-tsaren kudade, Dakta Mohammed Musa Tumala, ya ce, “Domin tabbatar da harkokin ciyo basuka na gudana bisa matakin da suka dace, kauce wa fadawa cikin hatsari da kuma shawo kansu.”
Ya ce, dole ne ya zama duk wani bashin da za a ciyo a yi nazari kuma a tabbatar an bi matakan ciyo bashi domin tabbatar da kiyaye matsalolin da ka iya janyowa a nan gaba.
Ana bin jihohi da gwamnatin tarayya basukan da suka kai naira tiriliyan 139, a rahotonnin da suke akwai.
A jawabinsa tun da farko, daraktan cibiyar hada-hadar kudade da tattalin arziki na Yammacin Afrika, (WAIFEM), Dakt Baba Y. Musa, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta maida hankali kan barazanar kara tara wa kanta basuka.