ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, November 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Gombe Ya Bayar Da Umurnin Raba Kayan Abinci Don Rage Raɗaɗin Kuncin Rayuwa

by Sulaiman and Khalid Idris Doya
1 year ago
Gombe

A wani mataki na daƙile ƙalubalen tattalin arziƙin da al’ummar Jihar Gombe ke fuskanta a halin yanzu, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da raba kayan abinci ga marassa galihu a faɗin jihar.

Hakan na zuwa ne bayan ƙudurin hakan da aka cimma a babban taron majalisar tsaron jihar da Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranta ranar Litinin kan matsalolin da zanga-zangar matsin rayuwa ya janyo a jihar.

ADVERTISEMENT
  • ‘Yansanda Sun Ja Hankalin Jama’a Kan Su Guji Rikiɗewar Zanga-zanga Zuwa Rikici A Ribas 
  • Gwamnatin Filato Ta Sassauta Dokar Hana Fita A Jihar

Don haka Gwamnan ya amince da raba buhunan dawa dubu masu nauyin kilogiram 50-50 da buhunan shinkafa dubu masu nauyin kilogiram 25 da katon dubu na taliya ga kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 11 na Jihar Gombe.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

Hakazalika, za a raba irin wannan tallafin abinci, buhuna 5,000 da katon-katon na taliya ga ƙungiyoyin addini, da ƙungiyoyin fararen hula, da ƙungiyoyin ɗalibai (GOSSA da NANS), da makarantun tsangaya da almajirai, da ƙungiyoyin matasa da mata da kuma masu buƙata ta musamman da sauran jama’a masu rauni a cikin al’umma.

Da ya ke karin haske kan wannan lamarin, kakakin gwamnan Malam Ismaila Uba Misilli ya ce wannan dai shi ne karo na 19 da gwamnatin jihar za ta raba irin wannan tallafi ga al’ummar Jihar Gombe a ci gaba da ƙoƙarin samar da agaji da inganta rayuwar al’ummar jihar a wannan mawuyacin lokaci.

“Ana sa ran tallafin abincin zai taimaka matuƙa wajen rage wahalhalun da jama’a da dama ke fama da su a jihar, musamman ma masu rauni.”

Ya kara da cewa, “Gwamna Inuwa Yahaya, ya ƙara jajircewa wajen aiwatar da ingantattun matakan tallafawa jama’a don sauƙaƙa musu rayuwa a tsaka da fama da ƙalubalen tattalin arziƙin da ake ciki.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7
Da ɗumi-ɗuminsa

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

November 15, 2025
Yanzu Satar Da Kuka Yi Ba Ta Da Amfani: Kwankwaso Ga Gwamnonin APC
Manyan Labarai

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

November 15, 2025
NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama
Manyan Labarai

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama

November 15, 2025
Next Post
Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Ketare Ya Karu Da Kaso 6.2 A Watanni 7 Na Farkon Bana

Cinikayya Tsakanin Sin Da Kasashen Ketare Ya Karu Da Kaso 6.2 A Watanni 7 Na Farkon Bana

LABARAI MASU NASABA

Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca

November 15, 2025
Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA 

November 15, 2025
Za A Yi Gwanjon Rigunan Messi Na Gasar Kofin Duniya Ta 2022 Da Kudi Tsagwagwa

Ina Son Kasancewa Cikin Koshin Lafiya Kafin Buga Gasar Kofin Duniya Na Shekarar 2026 – Messi

November 15, 2025
Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci

November 15, 2025
Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

November 15, 2025
Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

November 15, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

November 15, 2025
An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka

An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka

November 15, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan 

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan 

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.