Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gabatar da hasashen kasafin kudin 2023 da yawansu ya kai N173,697,242,000.00 ga Majalisar Dokokin Jihar.
Da yake gabatar da kasafin a gaban majalisar, gwamna Inuwa Yahaya ya ce, hakan na daga cikin muradinsu na hidimta wa al’ummar jihar har bayan 2023.
- Sauya Kudi Kokari Ne Na Haramta Amfani Da Naira – Sunusi Ata
- Yadda Maulidin Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Reshen Sakkwato Ya Gudana A Bana
Ya yi bayanin cewa Naira biliyan 71.8 kwatankwacin kaso 41.4 na kasafin an ware ga bangaren gudanar da ayyukan yau da kullum, yayin da kuma naira biliyan 101.8 kwatankwacin kaso 58.6 aka ware wajen gudanar da manyan ayyuka.
Gwamnan ya ce, a kasafin an yi nazarin samun kudaden shiga na yau da kullum da kason da jihar ke samu wajen tsarawa da fitar da kasafin.
Kana an saurarin bahasin jama’a domin Jin bukatunsu kafin fitar da kasafin.