Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya jaddada kudurinsa na fadada harkokin gwamnatinsa na fasahar zamani don tabbatar da cewa ilimin zamani ya samu cikin sauki a yunkurinsa na samar da kyakkyawar makoma ga matasan Jihar Gombe a duniyar yau mai saurin ci gaba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a sakonsa ga al’ummar jihar, yayin da ake alamta bikin ranar matasa ta duniya ta bana a wata sanarwar mai dauke da sanya hannun kakakinsa Isra’ila Uba Misilli.
- Kudaden ‘Yan Majalisa: Wa Za A Gaskata Tsakanin Hukumar Albashi Da Kawu Sumaila?
- Super Falons Ta Cigaba Da Zama Ta 36 A Jadawalin Iya Taka Leda Na FIFA
Ya ce taken ranar ta bana, “Daga Latsawa Zuwa Ci Gaba: Dabarun Zamani Ga Matasa Don Ci Gaba Mai Dorewa,” ya yi daidai da kudurin gwamnatinsa na tallafawa matasa ta hanyar Kirkire-kirkiren zamani.
Gwamna Inuwa Yahaya ya jaddada cewa gwamnatinsa tana ci gaba da maida hankali a fannin ilimi, da koyar da sana’o’i, da kasuwanci, da samar da ayyukan yi, tare da bunkasa wadata ga matasa da samar musu kayan aikin da suke buata don damawa da su a duniyar zamani. Ya kara da cewa, wadannan yunkuri suna da muhimmanci ga hangen nesan samar da makoma mai dorewa ga matasan jihar dana kasa baki daya.
Gwamna Inuwa Yahaya, ya ce gwamnatinsa ta kaddamar da wassu shirye-shiryen zamani don bai wa matasa sana’o’in hannu da nufin bunkasa fasaharsu a duniyar zamani. Daya daga cikin wadannan manyan shirye-shiryen shine na yin ayyuka ga kamfanonin kasashen waje daga nan gida Nijeriya wato Outsource to Nigeria Initiatibe (OTNI), inda aka ba da gudummawar cibiyar koyon sana’o’i da kudade don hadaka fasahar sadarwa don tallafawa matasa 2,000 da aka horar kan fasahar zamani da samar musu ayyukan yi.
Ya yaba da jajircewa da kirkire-kirkiren da matasa suke yi wajen kawo sauyi mai ma’ana a cikin al’umma, inda ya jaddada muhimmiyar rawar da fasahar zamani ke takawa wajen kyautatawar gobe, ya kuma bukaci matasan su rungumi damammakin fasahar zamani don sarrafa iliminsu wajen bada tasu gudunmawa ga jihar da samar da ci gaba mai dorewa.
“Matasanmu ba shugabannin gobe ba ne kawai, su ne ma masu kawo canji a yau, idan suka samu kayan aiki da damammakin da suka dace, za su iya cimma dimbin nasarori. Tare za mu gina Jihar Gombe inda kowane matashi zai iya sarrafa fasahar zamani zuwa ci gaba, da kuma burukanmu baki daya.”