Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kaddamar da motoci 150 da babura 500 da aka saya domin rabawa jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.
Gwamna Sani a yayin taron, ya bayyana cewa, ya fahimci kalubalen da jami’an tsaron ke fuskanta a jihar, musamman ta fannin zirga-zirga da kuma saurin kai dauki lungu da sako.
- Ɓata-gari Sun Lalata Hasumiyar Wutar Lantarki 3 Na Layin Biu-Damboa
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2 Daga Daliban Da Suka Sace A Kogi
Ya kuma sake nanata kira, da a sake duba dokar kaddamar da ‘yansandan Jiha.
Da yake jinjinawa jami’an tsaron da suka rasa rayukansu a kokarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar, Gwamna Sani ya ce, “Ba za a taba mantawa da jaruman ba, a saboda haka, na umarci ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta sanya wa dakin taro na ma’aikatar sunan Laftanar. Kanar AH Ali, wanda ya yi aiki tare da bayar da gudunmawa sosai wajen tabbatar da tsaro a Jihar Kaduna a lokacin da yake rike da mukamin kwamandan runduna ta musamman ta 198, kafin daga bisani a mayar da shi yankin Kudu-maso-Kudu, inda shi da hafsoshi da sojojinsa suka rasa rayukansu. Allah ya gafarta musu.”
A nasa bangaren, babban hafsan sojin kasa, Janar Chris Musa ya yabawa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa tallafin ababen hawa ga hukumomin tsaro.