Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, ya taya tsohon Gwamnan Kano, jagoran Kwankwasiyya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, murnar cika shekaru 67 a duniya.
Cikin wata sanarwar mai taken: Taya madugu Uban Tafiya murnar cika shekaru 67 da haihuwa, wacce mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a safiyar Asabar, 21 ga Oktoba, Gwamna Abba ya jinjina wa Kwankwaso bisa kishin al’umma, jagoranci nagari da aiki tuƙuru da ya yi fice a kai.
- Saboda Kishin Ilimi Muka Raba Wa Makarantun Kano Littafai Sama Da Miliyan 2 – Kwamishinan Addini
- Babbar Matsalar Nijeriya, Rashin Shugabanci Nagari – Wike
“A madadin al’ummar Jihar Kano, mai Girma Gwamna, Injiniya Abba Kabir Yusuf na cike da farin cikin taya shugabanmu, madugunmu kuma hasken fitilarmu – Mai Girma Sanata Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso PhD, FNSE, murnar cika shekaru 67 masu albarka a duniya.”
Abba ya jaddada cewa, Kwankwaso mutum ne nagari, mai aƙida ta ƙwarai, juriya da hangen nesa.
“Kyakkyawar aƙidarka ta gina al’umma, babban misali ne abin koyi ga dukkan shugabannin wannan zamani.
“Nasarorin da ka cimma da ayyukan da ka aiwatar sun tabbatar da kyakkyawar aƙidarka ta kishin al’umma da tsayin-daka kan nagartacciyar turbar siyasa, domin sadaukar da kai ga jiharmu da ƙasa a kowane lokaci.”
Daga nan sai gwamnan ya yi addu’a Allah ya ƙara wa Kwankwaso lafiya da ƙarfin hali da hikimar ci gaba da yi musu jagoranci, har ya dangana ga ƙololuwar nasara nan ba da daɗewa ba.