Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai gana da shugaban kungiyar ‘yan fansho, (NUP) na Jihar Kano, Kwamarade Salisu Ahmad Gwale kan zargin bacewar zunzurutun kudi har naira biliyan biyar.
Ana zargin kudaden ‘yan fanshon tun daga 2016 zuwa 2023 da suka kai kimanin naira biliyan biyar da dugo hudu, sun bace ne daga asusun kungiyar na Jihar Kano.
- A Magance Rashin Aikin Yi A Tsakanin Matasa
- An Kaddamar Da Cibiyar Buga Muhimman Takardu Ta AU Da Sin Ta Ba Da Taimakon Ginawa
Yanzu haka dai, gwamnan Jihar Kanon; injiniya Abba Kabir Yusuf ya gayya ci shugaban, sannan babu shakka makasudin wannan ganawar bai wuce tattauna batun bacewar wadannan kudade na fansho ba.
Kwamarade Gwale ya bayyana gamsuwarsa ga abin da gwamnatin Kano ta yi na tausaya musu da kaddamar makudan kudade da suka kai biliyan shida da gwamnatin ta ware domin biyan ‘yan fansho hakkokinsu.
Da yake jawabi, gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wannan ranar tana daya daga cikin ranakun farin cikinsa da ba zai taba mantawa da ita ba kan wannan dama da Allah ya ba shi na cika wasu daga cikin alkawuran da ya yi wa al’ummar Kano a lokacin gangamin zabe.