Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umaru Radda, ya nuna matukar takaicinsa kan yadda wasu ‘yan kasuwa a jihar ke boye kayan masarufi, musamman shinkafa sakamakon rufe iyakokin wannan kasa.
Radda, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanawa da Kakakinsa Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar a jihar, inda gwamnan ya yi nuni da cewa wannan dabi’a ta ‘yan kasuwa ba karamar abar kaico ba ce, musamman ganin yadda gwamnati ke nuna damuwarta kan yadda kayan masarufi ke ci gaba da yin tashin gwaron zabi a jihar.
Ya kara da cewa, sakamakon tashin farashin kayan masarufi a jihar ne ya sanya, kwanakin baya gwamnatin jihar ta amince da fitar da hatsi da takin zamani kimanin buhu dubu 39, 100, don raba wa masu karamin karfi da sauran manoma kyauta, don rage musu radadin kuncin halin rayuwar da suke ciki.
A cewar tasa, Gwamnatin Jihar ta lura wasu daga cikin ‘yan kasuwar jihar na boye kayan masarufi, domin haifar da karancin a fadin su a jihar, wanda hakan kan jawo tashin farashin nasu.
“A kwannan baya gwamnatin jihar ta amince da fitar da hatsi da takin zamani, don raba wa marasa karfi da manoma, musamman kanana da ke fadin jihar akalla buhunhunan hatsi dubu 39,100 kyauta, don rage musu radadin kuncin rayuwa”, in ji shi.
Radda ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa ko kadan ba za ta lamunta tare da saurara wa ire-iren wadannan ‘yan kasuwa marasa kishi da tausayin talakawa ba, za kuma su ci gaba da sanya idanu a kansu domin dakile ci gaba da afkuwar hakan.
“Mun lura wasu ‘yan kasuwa a jihar na boye kayan masarufi domin haifar da karancin abinci a wannan jiha, wanda hakan zai matukar jawo tashin farashinsu matuka gaya.”
A karshe, gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su mayar da hankali wajen sanar da mahukunta a fadin jihar sahihan bayanai a kan ire-iren wadannan ‘yan kasauwa marasa kishi da ke yi wa Gwamnatin Jihar zagon kasa na yunkurinta na samar da abinci a kan farashi mai sauki.