Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya kaddamar da aikin gina titi a Garin Argungu wanda zai lakume kusan Naira biliyan 7.23
Kamfanin Amirco Universal Concept LTD ne zai yi kwangilar wacce ake sa ran kammala ta cikin watanni 12 masu zuwa.
- Babu Shirin Rushe Babban Masallacin Jalingo – Gwamnatin Taraba
- Ban Ji Dadin Abin Da Libya Ta Yi Wa Super Eagles Ba – Tinubu
Jimlar tsarin gudanar da aikin shine kamar haka: Tagwayen Hanyoyi na Tsohon Bye-Pass aka Naira Miliyan 6.83; Mayar da Bututun Samar da ruwan Sha da aka binne a kasa kafin shimfida Titin, akan Naira miliyan 63.92; Biyan diyyar Gidajen da aikin titin ya biyo ta kansu akan Naira Miliyan 339.91
Kwamishinan Ayyuka, Hon. Abdullahi Umar Faruk Muslim, ya yabawa Gwamna Idris bisa yadda ya mika aikin ga fitaccen kamfani don tabbatar da cewa, an gudanar da aiki mai inganci.
A nasa jawabin, Mai martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad Mere, ya nuna jin dadinsa ga Gwamnan bisa cika alkawuran da ya dauka a yakin neman zabensa na gina tituna a dukkan masarautu hudu da ke jihar Kebbi.
Gwamna Idris ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta cika kashi 60 cikin 100 na alkawurran da ta yi wa masarautar Argungu dangane da samar da ayyukan more rayuwa. Ya kuma bayyana shirin bayar da kwangilar gyaran babban asibitin Argungu, bisa la’akari da halin da ya ke ciki a halin yanzu.
Wannan aiki na daga cikin kokarin Gwamna Idris na inganta rayuwar al’umma a fadin jihar Kebbi.
Kwanan nan ya kaddamar da aikin gina hanyoyin karkara a babbar hanyar Yauri/Hundeji da ke karamar hukumar Shanga.