Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya bukaci sabbin ‘yan majalisar dokokin jihar da su hada kai, su yi aiki don samun nasarar ayyukansu.
Lawal ya yi wannan roko ne a jiya Talata a lokacin da yake ganawa da sabbin ‘yan majalisar a fadar gwamnatin jihar.
- Daular Sakkwato Ta Buga Littattafan Malaman Musulunci Miliyan 3.2 —Sarkin Musulmi
- Dalilin Da Ya Sa Muka Rushe Shataletalen Gidan Gwamnati —Gwamnatin Kano
A jiya ne majalisar dokokin jihar ta kaddamar da mambobinta a zamanta na shugabanci bakwai tare da zabar shugabanninta kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.
Honarabul Bilyaminu Ibrahim Moriki (Zurmi ta Arewa) a matsayin shugaban majalisar karo na bakwai.
Ya bukaci ‘yan majalisar da su ci gaba da kulla kyakkyawar alaka da bangaren zartarwa na gwamnati.
Gwamna Lawal ya ce, “Ina so na yi amfani da wannan damar domin taya ‘yan majalisa 24 murnar kaddamar da su a yau.
“Haka kazalika Zamfara na fuskantar manyan kalubale da suka hada da rashin tsaro matsalar ilimi, kasuwanci da dai sauransu.
“Yanzu siyasa ta kare, lokaci ya yi da za a hada kai don kawo wa Jihar Zamfara ci gaba.”
Tun da farko, kakakin majalisar, ya ce ‘yan majalisar za su bayar da cikakken goyon baya tare da bayar da hadin kai ga bangaren zartarwa domin ci gaban jihar.