Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau na 16.
Ya gaji mahaifinsa, marigayi Dokta Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Yuli bayan ya yi shekaru 10 a kan karagar mulki.
- Tsohon Ɗan Takarar Mataimakin Gwamnan Kaduna Na PDP Ya Koma ADC
- EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Akwa Ibom
Masu zaɓen sarki a masarautar Gusau ne suka zaɓe shi bisa al’ada da dokokin ƙasa.
Kafin naɗin, Alhaji Abdulkadir yana riƙe da sarautar Bunun Gusau.
Shi ɗan Malam Sambo Dan Ashafa ne.
Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna, tare da roƙon Allah Ya bashi hikima da ikon yin jagoranci na gari.
Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da bin kyawawan ɗabi’u da tafarkin tsofaffin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Gusau.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp