Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayar da umurnin dakatar da duk wani nau’in cirar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba daga albashin ma’aikatan jihar.
Wannan ya biyo bayan da Ma’aikatan Zamfara suk koka tare da ƙorafe-ƙorafe da dama dangane cire-ciren kuɗi da ake yi musu a tsarin biyan albashin jihar.
- Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Atamfar Haɗin Kan Ƙasa Da Tallafin Littafi 50,000 A Zamfara
- Kotu Ta Hana CBN Da Sauransu Yi Wa Kudaden Kananan Hukumomi Katsa-Landan
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau, ya bayyana cewa umurnin da aka bayar ya haramta duk wani nau’in cirar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba da ake yi ta hanyar biyan albashin gwamnatin Jihar Zamfara.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A cikin ƙudirinsa na tsaftace tsarin biyan albashin ma’aikatan jihar Zamfara don samun ingantaccen tsarin biyan albashin su a adaidai lokacin da suke fuskantar cire-ciren kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, Gwamna Dauda Lawal ya bayar da umarnin dakatar da duk wasu bangarori da ba sa bin doka da oda wajen zaftare wani sashi daga albashin ma’aikata.
“An yanke hukuncin ne saboda ƙorafe-ƙorafen da ake yi na cire-ciren kuɗi daga albashin ma’aikata, inda ake zaftare wasu kuɗaɗen da sunan wasu ƙungiyoyin haɗin gwiwa na ‘Cooperatives’, wasu kuma da sunan biyan wasu basukan kayayyaki.
“Gwamna Lawal ya umurci kwamishinan kuɗi da ya dakatar da duk irin wannan cire-cire daga albashin ma’aikata tare da isar da umarnin ga duk ƙungiyoyin haɗin gwiwa da sauran masu sayar da kayayyaki.
“Don ƙarin haske, bangarorin da aka yarda kaɗai su cire kuɗi su ne: PAYE; Kuɗin ƙungiya; NHF; ZAMCHEMA; kuɗin amfani da ruwa; FMB (Hayar Gida kafin Mallaka); FMB (Gyarar Gida); Kuɗin hannun jari.
“Gwamnatin da ke yanzu a jihar Zamfara ta himmatu wajen aiwatar da matakan da za su taimaka wa walwala da ci gaban ma’aikatan ta. Wannan ya haɗa da haɓaka yanayin aiki, samar da albarkatun da suka dace, da kuma samar da yanayi mai kyau don tabbatar da ƙwararewar ma’aikata wajen gudanar da ayyukan su.