Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya yi naɗe-naɗen farko na waɗanda za su taimaka masa wajen tafiyar da gwamnati.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abubakar Nakwada ne ya sanar da haka a wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman kan Hakokin Kafafan sadarwa na zamani ga Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya sanya wa hannu kuma ya raba wa manema labarai a ranar Mayu 30, 2023 a Zamfara.
Sulaiman ya ce, gwamnan ya naɗa Alhaji Abubakar Nakwada a matsayin sakataren gwamnatin jihar (SSG). Haka kuma ya naɗa Mukhtar Lugga a matsayin Shugaban Ma’aikata.
Ya ƙara da cewa, “gwamnan Jihar ya kuma amince da naɗin Sharifudden F. Jatto a matsayin Babban Sakataren Gwamna; Imran Rufa’i Ahmad, a matsayin Mataimaki na Musamman ga Gwamna, Aminu Almajir a Matsayin Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gudanarwa; Sulaiman Bala Idris a matsayin Babban Mataimaki na Musamman kan Hakokin kafafen yaɗa labarai.”
“Sauran su ne Nura Almajir a matsayin Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Siyasa; Zahradeen Bello Imam, Babban Mataimaki na Musamman kan Al’amura; Pharm Abdulmajid Anka, Babban Mataimaki na Musamman a Ofishin Gwamna; Mustapha Jafaru Kaura, Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa labarai da Hulɗa da Jama’a; Faruk Ahmad Shettiman Rijiya, Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai; Kabiru Lawal Muhammad, Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Cikin Gida; Shamsuddeen Ibrahim, babban mataimaki na musamman kan harkokin cikin gida; Ali Akilu Bungudu, babban mataimaki na musamman kan harkokin tattalin arziki; da kuma Babangida Bisu a matsayin mataimaki na musamman kan yarjejeniya”, in ji sanarwar.