Dangane da halin da ake ciki a kasar nan da kuma kara kiraye-kirayen gudanar da zanga-zangar adawa da yunwa da tsadar rayuwa a ranar 1 ga watan Agusta, gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan Nijeriya da su kara hakuri, tana mai tabbatar musu da cewa, ana kokarin magance matsalolinsu.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada cewa, gwamnati na aiki tukuru domin warware matsalolin da ake fuskanta.
- Sakataren Gwamnati Da Ministoci Na Ganawar Sirri Kan Zanga-zangar Matsin Rayuwa
- ACF Ta Koka Da Rashin Tsaro Da Talauci A Arewa
Da yake magana bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja a ranar Laraba, Idris ya bayyana zanga-zangar da aka shirya a matsayin “matsala ce ta cikin gida” da za a warware ta don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin Nijeriya.
“Mun taru ne domin tattauna muradun kasa, kun ga cewa, wannan taro yana gudana ne a ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), wanda ministoci da dama sun hallara, suna aiki tare domin ci gaban Nijeriya.” Inji Idris.
Yayin da yake jawabi game da zanga-zangar da aka shirya yi, Idris ya amince da korafe-korafen, amma ya bukaci a kwantar da hankula, yana mai jaddada cewa, jami’an gwamnati ma sun dukufa wajen ganin an samu saukin rayuwa a kasar.
“Wadanda ke kokarin tayar da zanga-zangar ‘yan uwanmu ne, ‘yan Nijeriya, wannan lamari ne na cikin gida, kuma muna lura da shi ta idon fasaha, muna fatan za a samu zaman lafiya,” inji shi.