Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta kashe kuÉ—i Naira miliyan 50 domin gyara motocin ‘yansanda 15 da suka lalace don karfafa masu gwiwar yaÆ™i da ‘yan ta’adda.
Shugaban ma’aikatan ofishin mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Malam Mukhatr Aliyu Saulawa, ya bayyana haka a lokacin da yake miÆ™a motocin ga rundunar ‘yansandan jihar.
- An Rufe Taron Ministoci Karo Na 13 Na Kungiyar WTO
- Kwaskwarimar Kundin Tsarin Mulki Zai Gyara Kura-kuren Da Aka Samu A Zaben 2023 – AbbasÂ
Ya ƙara da ce gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Raɗɗa ne, ya amince da kashe waɗannan kuɗaɗen domin aiwatar da gyaran motocin.
“Wannan aiki na gyaran waÉ—annan motoci ya biyo bayan rokon da rundunar ‘yansandan ta yi ta hanyar Kwamishinan ‘yansandan Jihar Katsina, Aliyu Musa wanda ya yi rokon gwamna Malam Dikko Umar RaÉ—É—a ya taimaka musu” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa sun gayyato kanikawa da musu tada komaÉ—ar mota daga makarantar koyon sana’o’i ta Katsina Youth Craft Village domin karfafa masu gwiwa a kan sana’arsu.
Shi ma da yake amsar motocin a madadin shugaban ‘yansandan Nijeriya da kuma Kwamishina, mataimakin Kwamishinan ‘yansanda, DC Ibrahim Sa’ad ya yi godiya ga gwamna Malam Dikko Umar RaÉ—É—a
Sannan ya bayar da tabbacin kudirin rundunar ‘yansandan wajen ganin an yi maganin matsalar tsaro a Jihar Katsina kuma ya bayar da tabbacin za a yi amfani da motocin kamar yadda ka’ida ta nuna.