Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin magance matsalolin da suka dabaibaye harkar sayayya a hukumomin gwamnati tare da ƙara inganta ayyuka a ma’aikatun gwamnati.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a Abuja ranar Laraba yayin ƙaddamar da Gidan Yanar Takardun Shaidar Sayen Kaya na Nijeriya da Hukumar Sayen Kaya ta Ƙasa (BPP) ta ƙirƙiro tare da haɗin gwiwar Bankin Duniya.
- Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar
- Wasu Kwamandojin ‘Yan Ta’adda Sun Miƙa Wuya A Katsina
Idris ya ce: “Wannan taron wata babbar alama ce ta ci gaba a ƙoƙarin da ake yi na sauya tsarin sayen kaya na gwamnati a Nijeriya, wanda ke da cikakken daidaito da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, musamman wajen ƙarfafa tsarin shugabanci domin isar da ayyukan gwamnati cikin inganci, gaskiya da riƙon amana.”
Ministan ya ce sabon gidan yanar na intanet zai taimaka wajen shawo kan matsalolin da suka daɗe suna dagula harkokin sayayya a gwamnati, kamar yadda ake fama da rashin ingantattun tsare-tsare, ƙarancin ƙwararru da rashin tsarin horaswa na dindindin.
Ya ce: “Ƙaddamar da wannan sabon shafin ba kawai cigaba ba ne a fannin fasaha; wata babbar hanya ce ta sauya fasalin aiki gaba ɗaya wadda ke magance manyan ƙalubale a tsarin sayen kaya na gwamnati, irin su cikas da ke yawan faruwa, rashin ingantattun hanyoyin sayayya, ƙarancin ma’aikatan da suka dace, da kuma rashin ingantaccen tsarin gina ƙwarewa.
“Waɗannan matsaloli sun daɗe suna hana a yi amfani da dukiyoyin gwamnati yadda ya kamata tare da kawo cikas ga cigaban tattalin arziki gaba ɗaya a ƙasar nan.”
Ya ce wannan sabon tsari zai bai wa jami’an sayayya damar samun horo, takardun shaida, da kuma damar yin aiki da ƙwarewa, daidai da matakin duniya.
Idris ya ce: “Za a tabbatar da cewa mu jami’an gwamnati muna sayen kaya ba kawai bisa doka ba, har ma ƙwararru ne kuma masu iya gogayya a matakin duniya.”
Idris ya yaba wa Darakta-Janar na BPP, Dakta Adebowale Adedokun, bisa jajircewa da hangen nesan sa wajen inganta tsarin sayayya a Nijeriya.
Ya ce wannan gidan yana hujja ce ta jajircewar sa wajen ganin an sabunta tsarin sayayya a ƙasar nan.
Ministan ya kuma buƙaci ‘yan ƙasa da su fahimci cewa sabon gidan yanar ba kawai don gwamnati ba ne, har ma wata hanya ce da za su iya amfani da ita wajen neman ingantattun ayyuka da gaskiya.
“Don haka ina kira ga dukkan hukumomi da jami’an gwamnati da su rungumi wannan shiri gaba ɗaya, kuma ina kira ga kafafen yaɗa labarai, musamman, da su taimaka wajen yaɗa amfanin sa da kuma sa ido kan yadda ake aiwatar da shi,” inji shi.
Cikin waɗanda suka halarci taron akwai Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Didi Esther Walson-Jack; Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Mista Wale Edun; Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa; Ministar Harkokin Mata, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim; Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa (rtd); da Darakta-Janar na FRCN da NTA, Dakta Mohammed Bulama da Kwamared Abdulhamid Dembos.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp