Gwamnatin Tarayya ta amince da kashe Naira Biliyan N110 don gudanar da ayyukan tituna cikin gaggawa a Jihohi 36 na Tarayya da babban birnin tarayya.
Ministan ayyuka Engr. David Umahi, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce shugaba Bola Tinubu yana sane da mummunan halin da hanyoyin kasar ke ciki tun hawansa karagar mulki.
- Nijeriya Ta Nanatawa Amurka Kudirinta Na Ci Gaba Baiwa ‘Yan Jarida ‘Yanci
- Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Da Su Tinkari Barazanar Dake Tattare Da yarjejeniyar AUKUS
Ya kara da cewa, tuni dama shugaba Tinubu ya fito da tsare-tsare na sadaukarwa, daidaito da kuma sabbin abubuwa don tabbatar da dorewar ci gaban ababen more rayuwa a fadin kasar nan.
Acewarsa, “shugaban kasa ya amince da karin kasafin kudi na shekarar 2023 na naira biliyan ₦300bn ga ma’aikatar ayyuka wanda za a kashe Naira Biliyan ₦110bn don ayyukan gyare-gyaren tituna cikin gaggawa a jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja da kuma Naira biliyan N200bn domin ci gaba da ayyukan da sabuwar gwamnatin ta gada daga wacce ta shude.”